YA KAI ƊANUWA
MAI GIRMA

✿ Ka ajiye wayarka
    ka yi shirin tafiya
    Masallachi.

✿ Ka zauna ka
    saurari huɗuba
    cikin nutsuwa

✿ Ka yi sani, idan
    Liman yana
    huɗuba, kai ko
    kana surutu, to
    fa baka da
    Juma'a

✿  Ko da ko hana
     wani surutu ko
     aikata wani aiki
     kai ma ka kayi
     Laghawu.

              via
DARUL📚ULOOM


http://darululoom099.blogspot.com/2017/10/tunatarwa-ya-kai-dan-uwa-mai-girma.html

Post has attachment
SALATUL JUMA'AH
• Its essentials
• Its rules
• Its adaabs
• Its kaifiyah ... and others
- 📚 Darul Uloom

http://darululoom099.blogspot.com/2017/10/salatul-jumaah.html

🇹🇺🇳🇦🇹🇦🇷🇼🇦 
SUNNONI DA LADUBBA
A RANAR
🇯🇺🇲🇦' 🇦🇭
============================
l بِسْـــــمِ اللَّـــهِ الرَّحْــــمَٰنِ الرَّحـــِيم l
❞ يَـٰٓأَيُّہَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا نُودِىَ لِلصَّلَوٰةِ مِن يَوۡمِ ٱلۡجُمُعَةِ فَٱسۡعَوۡاْ إِلَىٰ ذِكۡرِ ٱللَّهِ وَذَرُواْ ٱلۡبَيۡعَۚ ذَٲلِكُمۡ خَيۡرٌ لَّكُمۡ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ ۝❝

Ya ku wadanda suka yi imani! Idan an yi kira zuwa ga Sallah a ranar Juma’a, sai ku yi aiki zuwa ga ambaton Allah, kuma ku bar ciniki. Wanda shi ne mafi alkhairi a gareku in kun kasance kuna sani

============================
📚 LET ME LEARN📚
============================

1⃣. GYARAN JIKI
✿ Yin wanka (irin na Shari’a):
❞ غسل الجمعة واجب على كل مسلم ❝
-📓 البخارى (2/6)، مسلم (6)

✿ Tsaftace haƙora (teeth) da aswaki ko da kayan goge baki na zamani (toothpaste & brush):

❞ لولا أن أشق على أمتي لأمرتهم بالسواك مع كل الصلاة ❝
-📓 المسلم (1/220)

✿ Sanya mafi kyawun tufafi, tare da sanya/fesa musu turare mai ƙamshi:

❞ على كل مسلم الغسل يوم الجمعة، ويلبس من صالح ثيابه، وإن كان له طيب مس منه ❝
-📓 الإمام أحمد (4/304)

2⃣. TAFIYA MASALLACI
✿ Tafiya Masallachin Juma’a da wuri:

❞ من اغتسل يوم الجمعة غسل الجنابة، ثم راح في الساعة الأولى فكأنه قرب بدنة...❝
-📓 البخارى (2/3)، الترمذى (499)

3⃣. YAWAITA AMBATO (ADHKAR)
✿ Yawaita Ambato Allah (Adhkar), i.e. Tahlili (لا إله إلا الله), Tashibi (سبحان الله), Tahmidi (الحمد لله), Takbiri (الله اكبر), Tilawar Alkur’ani Maigirma dss:

❞ يَـٰٓأَيُّہَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا نُودِىَ لِلصَّلَوٰةِ مِن يَوۡمِ ٱلۡجُمُعَةِ فَٱسۡعَوۡاْ إِلَىٰ ذِكۡرِ ٱللَّهِ...❝
-📓 سورة الجمعة، الأية 9

✿ Yawaita yiwa Annabi (ﷺ) Salati:

❞ أكثروا علي من الصلاة يوم الجمعة ولية الجمعة، فمن فعل ذلك؛ كنت له شهيدا وشفيعا يوم القيامة ❝
-📓 الحاكم (2/421)، البيهقي (3/249)

✿ Karanta Suratul Kahf:

❞ من قرأ سورة الكهف فى يوم الجمعة؛ أضاء له من النور ما بين الجمعتين ❝
-📓 الحاكم (1/511)

✿ Yawaita Addu’a:

❞ إن في يوم الجمعة لساعة لا يوفقها عبد مسلم يأل الله عز وجل فيها خيرا إلا أعطاه إياه ❝
-📓 إلاما أحمد (2/185)

4⃣. LADUBBAN SHIGA MASALLACHI

✿ Shiga Masallachi da ƙafar 👢dama.
- 📓 آدب المشي إلي الصلاة

✿ Addu’a yayin shiga Masallachi:

أَعُوْذُ بِاللَّهِ الْعَظِيمِ، وَبِوَجْهِهِ الْكَرِيمِ، وَسُلْطَانِهِ الْقَدِيمِ، مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ [بِسْمِ اللَّهِ، وَالصَّلاةُ] [وَالسَّلامُ عَلَى رَسُولِ اللَّهِ] اللَّهُمَّ افْتَحْ لِي أَبْوَابَ رَحْمَتِكَ
- 📓 أبو داود (1/318، النووي في الأذكار، ص: 26، مسلم، (1/494)

✿ Yin Nafila ta gaisuwar Masallachi (Tahiyatul Masjid) raka’a biyu, marasa nauyi ko da ko Liman yana cikin yin huduba:

❞ إذا دخل أحدكم يوم الجمعة والإمام يخطب فليركع ركعتين وليجوز فيهما ❝
-📓 الإمام أحمد (2/303)

5⃣. LADUBBAN ZAMA A MASALLACHI DOMIN SALLAR JUMA’A
✿ Zama da nutsuwa da sauraron hudubar liman. Sannan idan liman yana huduba an haramtawa kowa yi magana ko da ko hani ne ga wani mai surutu ne domin yayi shiru:

❞ من مس الحصى فقد لغى، ومن لغى فلا جمعة له ❝
-📓 أبو داود (1050)
============================
سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، أَشْهَدُ أَنْ لاإِلَهَ إلاّ اللَّه، أَسْتَغْفِرُكَ وَأَتُوبُ إِلَيك

©
🇩 🇦 🇷 🇺 🇱 📚🇺 🇱 🇴 🇴 🇲
WHATSAPP GROUP


http://darululoom099.blogspot.com/2017/10/tunatarwa-sunnoni-da-ladubban-jumaa.html

Post has attachment
MAIMUNATU BINT AL-HARITH
(ميمونة بنت الحارث)
" Ita ce mata ta karshe a gidan Manzon Allah ﷺ "
-


.
Sunanta Maimuna (ميمونة) bint al-Haris (الحارث) bn Hazn (الهزم) Al-Hilaliyya (الهلالية), sunan mahaifiyarta Hind bint Awf (هند بن عوف) ‘yar qabilar Himyar ta Yemen. Maimunatu bint al-Harith ta kasance 'yar uwar Ummu Fadal (أم فضل). An haifeta a kafin Hijira da shekara 28 a garin.
- Al-Isaba 8/192

Asalin sunanta Barratu (برّة) sai Manzon ﷺ Allah Ya canza mata suna zuwa Maimuna (ميمونة) ma’ana ‘Mai albarka'. Kafin ta auri Manzon Allah ﷺ ta auri Mas'ud bn Amr Athaqafy (مسعود بن عمور الثقفى) tun a lokacin Jahiliya (kafin zuwan Musulunci) sai suka rabu. Bayan nan sai ta auri Abu Ruhum bn Abdul Uzza (أبو رهم بن عبدالعزى) shi kuma rasuwa (mutuwa) yayi. Bayan rasuwarsa ne sai ta auri Manzon Allah ﷺ a lokacin da akayi Umarar Ramuwa (عمرة القضاء) a watan Dhul-Qa'adah shekara ta bakwai (7) bayan hijira a Sarif wanda yake da tazarar mil goma (10) tsakaninsa da garin Makkah, a lokacin tana ‘yar shekara 58 a duniya.

Muhammad bn Umar yace ita ce ta bayar da kanta ga (ta nemi auran) Manzon Allah ﷺ sai Ya aureta a hannun baffansa Abbas akan sadaki dirhami dari biyar (500) kamar yadda Ibn Sa'ad (ابن سعد) ya fitar daga Abdullah bin Abbas Yace "Manzon Allah Yace 'yan uwa guda hudu (4) muminaine; Maimuna da Ummu Fadal أم الفضل لبابة الكبرى الهلالية (mahaifiyar Abdullah bn Abbas) da Asma'u bint Umays أسماء بنت عميس(matar Abubakar R.) da Salma bint Umays سلمى بنت عميس (matar Hamza ibn Abud al-Muttalib).

Kasancewarta matar Manzon Allah ﷺ Ya sanya ta zama malama dake ruwaitu hadisai daga Manzon Allah ﷺ Imamuzzahabi yace "an ruwaitu hadisai goma sha uku 13 daga gareta.
- Siyaru 2/240; Tarikul Rasul wal-Muluk, 201

Ibn Sa’ad yace tarasu daga wakidiy yace ta rasu tana da shekaru 80 ko 81 a shekara ta 51 bayan Hijirar Annabi ﷺ daga Makkah zuwa Madinah zamanin Mulki Yazid dan Mu’awiyyah. Kuma itace karshen rasuwa cikin matan Manzon Allah ﷺ.

Amma Imamuz-Zahabi yace bata kai wannan lokacin ba lallai ta rasu kafin Aisha, yace ita ce ta rasu a shekara ta 51 bayan Hijira, bayan ta dawo daga aikin Hajji, kuma dan ‘yan uwarta (أم الفضل لبابة الكبرى الهلالية) Abdullahi bin Abbas (R) Ya sallace ta Allah. Ya kara mata yarda.
- Al’isaba 8/192, Siyaru ‘alamin Nubala 2/239-245, Alhakim: Mustadark 4/32

To be continued… in sha Allah

✍ Mal. Ka'ab Saleh
21st Muharram, 1439AH
12th October, 2017CE

http://darululoom099.blogspot.com.ng/2017/10/tarihin-sahabbai-mata-1-maimunatu-bint.html

Post has attachment
📝 🇨 🇭 🇦 🇳 🇯 🇦 📝
SUNAN GROUP DAGA
🇱🇪🇹 🇲🇪 🇱🇪🇦🇷🇳
ZUWA
🇩 🇦 🇷 🇺 🇱 🇺 🇱 🇴 🇴 🇲
19011439AH | 10102017CE

Assalamu Alaikum

Group ɗin LET ME LEARN an ƙirƙireshi tun ranar 19th April, 2015 (shekara 2 da watannin 4 da sati 2 da kwanaki 3 a yau), wanda a tsari na Onomastic, an haɗa sunan group ɗin da kalmomin Turanci guda uku LET, ME da kuma LEARN wanda ke nufi BAR NI IN KOYA/SANI a Hausance. Muna gudanar da harkokin group da suka shafi ilimi zalla a cikin group ɗaya (1), daga baya da mutane suka yi yawa (group ɗin ya cika) sai aka buɗe Group 2, aka buɗe Group 3 (na mata), wanda a yanzu haka group yana da members guda 340 (Group 1: 172, Group 2: 72 & Group 3: 96).

Bayan karɓar shawarwari daga ƴan uwan, yayu kuma iyaye masana masu nazari akan sanya suna da alaƙa (Onomatology/علم الأسامي) da kuma tsarin ƙungiyoyi (I/O Psychology/الحالة العاطفية الجماعية) wajen sabunta sunan group/المجموع ya koma wanda zai haɗa kowannen ɓangare (na malamai da almajirai) da masu nazariyyat daban-daban bisa hujjoji na ilimi (Textual proofs/الأدلة النقلية) da na hankali (Rational Proofs/الأدلة العقلية) da kuma nazari abin da hakan zai haifar ana gaba (Futurology/علم المستقبلياتا) in shaa Allah.

🇩 🇦 🇷 🇺 🇱📚🇺 🇱 🇴 🇴 🇲

DARUL ULOOM (دار العلوم) kalmomin larabci () ne biyu (compound; دار da kuma العلوم). DAARUN (دارٌ) a yare yana nufin gida (house), AL-ULOOM (العلوم) jam’in (plural) kalmar ILM (علمٌ), ma’ana ilimi/sani. Idan muka hadesu za su ba mu DARUL-ULOOM (Gidan Ilimi/House of Knowledge) kuma shi ne sunan da muka zaɓa domin sabunta (change of name/تغيير الاسم) na group ɗin LET ME LEARN, kuma in shaa Allah dukkan posting ɗinmu na gaba (future postings) za suna fita da sunan DARUL ULOOM .

Daga cikin sauye-saye na cigaba da muka samu, mun buɗe blogsite na kamfani google (darululoom099.blospot.com), page a shafin Facebook (facebook.com/darululoom099), shafi a Manhajar Twitter (https://mobile.twitter.com/DarulUloom5), Group a Manhajar Telegram (https://t.me/joinchat/Eo2RxwrLOAvxBMesMgaVfA) da kuma shafi a Google+ (https://plus.google.com/107339910879266272280). Sannan a jiya an buɗe sabon Email na group (darululoom099@gmail.com)

Daga cikin sabbin tsare-tsaren group, akwai haɗa kacici-kacici (Quiz/المسابقة), filin muharawara da tattaunawa (debate & discussion/المناقشة) kan wasu masa'il na rayuwa ko na addini da sauraransu lokaci-zuwa-lokaci in shaa Allah.

A ƙarshen muna fata da kuma roƙon Allah Ya sakawa kowa da alkhairi, Ya ƙara sanya mana albarka cikin rayuwarmu musamman ta ɓangaren karatu, Ya bamu iko da dama amfana da duk wani tsari da aka kawo mana na cigaba amin


Signed:
🇩 🇦 🇷 🇺 🇱 📚🇺 🇱 🇴 🇴 🇲
WHATSAPP GROUP

http://darululoom099.blogspot.com/2017/10/chanja-sunan-group-daga-let-me-learn.html

📜 🇹🇦🇷🇮🇭🇮🇳   📜
🇸🇦🇭🇦🇧🇧🇦🇮 ( 🇷)
1⃣

MU'AZ BIN JABAL (R)
l معاذ بن جبل l


"...وأعلمهم بالحلال والحرم معاذ"
"Mafi sanin Al'umma halal da haram shi ne Mu'az bin Jabal"
📚 Tirmizi 3793, Ahmad 3/184


Sunansa Mu'az bn Jabal bn Amr bn Aus bn A'iz bn Ka,ab. Ana yi masa alkunya da Abu Abdurrahman Al'khazrajiy Al'Ansariy
📚 Al Isabah

Ya halarci caffar Aƙaba tare da mutanen Madina lokacin da aka yi Hijirah zuwa Madina, Manzon Allah ﷺ Ya hada shi 'yan uwantaka da Abdullah bin Mas'ud, ko da yake Ibn Ishaq ya ce 'an hada shi ne da Ja,afar bin Abi Dalib.

Ya halacci Yakin Badar da dukkanin yakoki tare da Manzon Allah.
📚 Bidaya

A shekara ta tara da Hijira, Manzon Allah ya tura shi zuwa kasar Yamen domin ya koyar dasu Addinin musulunci Mu'az bai dawo ba sai da Manzon Allah ﷺ Ya rasu

Mu'az yana daga cikin manyan sahabbai da suka samu fahimtar Addini. Abdullah dan Umar yana cewa Manzon Allah ﷺ yace:

"خذوا القرآن من أربعة: من ابن مسعود، وأبيّ، ومعاذ بن جبل، وسالم مولى أبي حذيفة"

"Ku koyi karatun Alqur'ani daga mutane hudu; Abdullah bin Mas'ud, da Ubayyu bin Ka,ab, da Mu'az bin Jabal da Salim Maula Abu Huzaifah"
📚 Bukhari 6/44

Mu'az ya rasu a annobar da ta sami musulmi a kasar Sham (Syria a yanzu) a shekarata ta sha takwas 18 bayan Hijirah yana tare da Abu Ubaidah Amir bn Jarrah (R.A.) a lokacin yana da shekara 33 ko da hudu
📚 Al-Muntazam 4/365, خلق المسلم للغزالي: ص١٣١، الطبقات لابن سعد ٣/١٢٤

Allah kaqara mana son sahabban Manzon Allah ka tashemu tare dasu kacire mana duk wani gilli.

To be continue... in shaa Allah


✍Mal. Ka'ab Saleh
20th Muharram, 1438AH
11th October, 2017CE


via:
🇩 🇦 🇷 🇺 🇱 📚🇺 🇱 🇴 🇴 🇲
WHATSAPP GROUP

http://darululoom099.blogspot.com/2017/10/tarihin-sahabbai-1-mu-bin-jabal-r.html
Wait while more posts are being loaded