Profile

Cover photo
Verified name
8,920 followers|10,031,023 views
AboutPostsPhotosYouTube

Stream

BBCHausa

Shared publicly  - 
1
Add a comment...

BBCHausa

Shared publicly  - 
 
Za a yi taron adu'oi a Paris http://bbc.in/1Q1R7Ab
 ·  Translate
1
Add a comment...

BBCHausa

Shared publicly  - 
2
Badamasi Aliyu Rijiyarlemo's profile photo
 
Allah dai yasa mudace
Add a comment...

BBCHausa

Shared publicly  - 
 
Russia za ta taya Faransa yakar IS http://bbc.in/1MHcuVp
1
adamu biyu biyar's profile photoBello Haro Magami f/samji's profile photoashiru sani's profile photoUmar Alassan Kamaru's profile photo
5 comments
 
To Allah yasa dai kwalliya ta biya kudin sabulu 
Add a comment...

BBCHausa

Shared publicly  - 
1
jamilu lalo's profile photo
 
Ya cancanta 
Add a comment...

BBCHausa

Shared publicly  - 
 
FIFA ta ba da agajin agoguna 48 http://bbc.in/1MGbOiQ
 ·  Translate
Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta ce ta bayar da gudunmawar wadansu agoguna 48 ga wata kungiyar agaji a harkar kwallon kafa.
1
adamu biyu biyar's profile photo
 
hmmm gaskiya FIFA kin taka rawar ganin a wannan zamani , Allah yabtaimake Ku ameen uppp isah hayatu
DAGA ADAMU BIYU BIYAR NGURU
Add a comment...
In their circles
9 people
Have them in circles
8,920 people
Ibrahim Aminu's profile photo
Abdulazeez Sulaiman's profile photo
Inuwa Daneji's profile photo
Ashiru saleh Baure's profile photo
Johnbiafra Inyari's profile photo
jamilu abdullahi's profile photo
Nuyong Elam's profile photo
Tasiu Garba's profile photo
Abubakar Dabo's profile photo

BBCHausa

Shared publicly  - 
 
Jirgin sama marasa matuki da zai rika sa ido kan bola http://bbc.in/1MHztiR
 ·  Translate
1
Add a comment...

BBCHausa

Shared publicly  - 
 
CI GABAN MACE MUTUM KASHI NA 26
Komai ya lafa saura zaman makokin, amma a gare ni kadaici bai gama ba. Ba ma a zuciyata ba, har a jiki. Domin kowa ya koma gidansa, saura ni. Ni ce ban koma Abuja, gidan mijina ba. Bai ce na koma ba, bai kuma zo ya dauko ni ba. Bayan kwana arba’in, ya zo ya ce ya saida wancan gidan, yana neman wani. Sai ya gyara sa’annan zai zo ya dauke ni, mu tare. A haka nake zaune wata biyu, uku... hudu.... har wata shida, iyaka dai wasu lokuta Yaya Bashir kan leko Kano don ganawa da lauyan Mama, akan abin da ta bari. Wannan kan sanya su zo gidan shi da lauya, wato barista Lawal. A wannan katon gida, ni ce ‘yar Mama, kuma ni ce matar danta daya tilo. Ina wakiltarta, ina wakiltar mijina. Wannan ya sanya ina da mulkin duk wanda ke karkashin gidan a hannuna, duk da cewa a wajen Bashir ni ba kowa ba ce, ban da mai tsaron gida, don haka ba ni da labarin ranar tashina.
Ba zan boye ba, ina cikin damuwa matuka, musamman don ganin kara zama alakakai da na yi . Ina da ta son sanin makomata a gaba, bayan da na sam matsayina na yanzu, amma na kasa. Ko da da cin fuskar juna, in mace na ganin wanda ya ajiye ta ko ma tana ji yana sane da shi ya ajiye ta, to da sauki.
Duk safiya Bashir kan bugo waya. Amma don ya ji lafiyar gida, ba don ya ji muryar matarsa ba. In ka ji ya damu da jin muryata to matsayin nan nawa ne ya motso, wato na mai abincin ban girma. Sai dai yanzu bakinsa ba su da yawa, domin mafi yawan lokuta Barista Lawal ne, wanda suka yi mutukar shakuwa da Bashir. Shakuwar da take da amfani a gare ni, kasancewar Barista Lawal na yawan zuga abincina da yaba mani a gaban Bashir da cewa lallai ya sami mace, wadda shi a dalilin rashin samun irina, har yau bai yi aure ba. Irin wannan zuga kan samo min fara’ar Bashir ta wucin gadi. Ga shi dai har yau lauya bai sabawa, in dai ya zo to sai ya nasabta wani abu me kyau da ni . Don haka ni ma na shaku da son ganinsa da bai wa ranar zuwansa muhimmanci. Domin na auna tabbas, in har zai zo, to ba zan kwana da bakin ciki ba a ranar.
Farin cikina ya karu a yayin da muhimmancina, ya karu wajen lauya, har ta kai yana yi mini wayar labarin maigida ma, har ta kai an koma gimbiya yaya kika kwana? Da sannu dai lauya ya soma zuwa taya ni hira ko da Bashir bai zo ba. Ya kan tara mutanen gida ya yi mana sayayya, sa’annan ya ci abinci, a yi hira, ya tafi, wani lokacin ma har ya buga Bashir waya su yi hira.
Na soma samin tsarguwa kan yawaita kallon da lauya yake man, wanda in na cika tsarguwa, sai ya ce, Gimbiya ke nan. Kina jin dadinki. Amma daga baya sai ya koma cewa, yana yawan karanto damuwa ne a fuskata, shi ya sa yake kallona da yawa, shin ko’ina da matsala, na gaya masa. Abin ka da masoyin mai tausaya wa, duk da ban taba fada masa ko ina da matsala ba, sai ina jin dadin tambayar da lallashinsa gare ni. Inda har ta kai wata rana yake cewa ko da ban amsa ba, ya riga ya sani ina da matsala.
Wasu ‘yan lokuta ya kan ba ni labarin munanan halayen mazan da ba su kula da hakkin matansu. Labarin da ba ni da zabi sai na tofa albarkacin zuciyata, ba na bakina kawai ba. Amma a karshe ya kan rufe zancen da gazawar Bashir wajen kula da wannan baiwa wato ni.
Da yake duk da a sashin barkwanci ake wannan zance, sai na rasa abin da zan ce da zai zamo amsa mafi daidai, kamar mai amsa laifi a kotu, na yi na’am da tsokacinsa kan Bashir. Don haka wata rana kawai sai ya ci gaba da cewa.
“Fati ko kin boye, na san ko waye Bashir a gare ki, miji ne wanda bai fitar da hakkinki, sa’annan ba ki da wata matsala sama da Bashir. To amma ko kin san asirin faruwar hakan?”
Ban ce E ba, ban ce A’A ba, amma kawowar idona a kansa ya isa ya nuna masa zakuwata da son sanin wannan asiri, don haka bayan dan jimawa yana karatun amsar, sai ya jefa hannu a aljihun ciki na kirjin kwat din shi, sai ya bar hannun ciki ya kuma duba na.
“Kodayake sai kin bude baki kin yi mini alkawarin ba za ki taba fada wa wani cewa ni na ba ki wannan bayani ba.”
“Na yi alkawari”, abin da na ji bakina na cewa ke nan.
Sai ya fito da wata ‘yar takarda, ya taso ya iso gabana ya mika mini.
“Ki je wannan wajen ranar litinin da misalin karfe shida na yamma. Duk ma’aikata sun tashi saura abin da za ki gani ki bude wannan wajen ki shiga.”
Sai da na gama jinsa, sa’annan na soma karantawa.
Gini me kallon otel din Daula. Hawa na uku, sashin dama. Ofis na biyu ta hagu.
Na dago na kalle shi da idon tambaya.
“Eh. Ba zan kara komai ba sai kin gane wa idanunki.”
* * * *
Zakuwa ce ta hana ni isashshen bacci har kwana uku sa’annan Litinin ta iso. Ban sha wahala wajen yarda da cewa za ni ganin kwakwaf ba, amma na sha wahala wajen tunanin ko me zan taras.
Tun biyar da rabi na iso ga wannan gini, kallonsa ya dame ni kamr yadda zuciyata ta dami bangon kirjina. Na dinga jin abubuwa, wani lokaci doki, wani lokaci tsoro, wani lokaci bugun gaba mara dalili.
Shida ta buga tare da zuciyata a yayin da na ji ina aikata umarni Lauya ba tare ina da wani hankalin tafi da gidanka ba. Na yi kasa don haka tun ina hawa a hankali sai na ji na karashe da sauri a yayin da na kusa isa wannan hawa.
Na bi tsarin dakunan, har na isa ga wanda nake bukata. Mahadar gwiwoyina a sace suke, don haka kafafuna ke rawa kamar za su tsinke. Na kalli kofar cikin faduwar gaba, wanda tuni kunne ya amsa, sa’annan ban san abin da ya sa na kwankwasa kofar ba, amma tun kafin na gama, sai na ji da ma bankadawa na yi na shiga. Ban gama da na sani ba sai da na ji muryar mijina ya ce. “Yes come in.”
Na murda na shiga ina dan karkarwa.
Cinyar mace fara kal, wadda kafafunta ke cikin bakin takalmi, sawu ciki mai tsini. Tana zaune bisa cinyar namijin da ba wani ba ne illa mijina, kuma Yaya Bashir, wanda ke zaune a kujerar bayan dimemen teburin rubutu da ke dauke da robar askirin din da take ba shi a baki. Yana cikin wata fara’a da rabo na da ganinsa da ita tun ba mu yi niyyar aure ba.
Duk sun juyo suka kalle ni da walwala, sa’annan firgita ta shige su na wasu dakiku, sa’annan suka girgije, har matar ta so ma yi mani kallon biyu ahu.
Girgijewarsu ta zo daidai da dawata daga hoton da na zama sakate, ina raba ido a kansu. Na soma hadiye dumbin yawun bakin ciki. Kodayake na san Bashir manemin mata ne. Amma ban taba kama shi ba, ban kuma taba zaton in na kama shi din zan yi mamakin a zo a gani ko wani bakin ciki ba, sai a yanzu.
Ji nake zuciyata tana konewa, kwakwalwata na atishawa da kararta ya cika duk wata kafar jini. Marata ta ja wani zare ya tsinke a cikina, ciwo ya haddasa. Ina tsaye kan kafafun da ba ni da tabbacin za su iya ci gaba da dauka ta.
“Me kika zo yi nan?”
Ya tambaye ni cikin harzuka. Duk da idanuna a kansa suke, amma ban ga lokacin da ya fara magana ba sai muryarsa na ji. Zuciyata ta kama in ina garin karafniya da amsa mafi dacewa.
“Shin za ki hanzarta bace mini da gani lo kuwa?”
Abin da yake cewa ke nan, fuskarsa dauke da fushin fin karfi, za ka iya gan cewa na gaskiya na gabansa, ba fin karfin ne a gabansa.
Na so yin magana, amma na kasa, na so tsayawa, shi ma na kasa. Ina hannun bakin cikin daban don zai taba mallakata ba har na fita, na maida kofa ba da shawarar zuciyata ba.
A gida, sai da kowa ya gane ina cikin damuwa, amma babu wanda ya gane ta mecece sai Hajiya Hasana, wadda na gaji, na gaya mata. Allah Sarki, babu ko da shawarar hanyar daukar fansa da na samu, sai cewa in yi hakuri, wannan shawara kuwa ko da zuciyata ba ta ba ni ita ba, ta yarda da ita a matsayin mataki kwaya daya da za ta iya bi. Wato ba ni kadai ba, mafi yawan matan zamani ko na birni, matakan da suke iya bi a faruwar irin wannan uku ne. Ko dai su dan dinga fushi, in suna da ‘yar kima wajen miji, ya zo ya yi lallashi, su dan ja aji na dakiku, sa’annan komai ya wuce. Ko kuma su ja rigimar da mafi yawa maimakon galaba sai dai su kwana ciki, wasu kuwa kallon mamaki da takaici za su dinga yi wa lamarin, ba um,ba um-um, har komai ya lafa su saba. Duk wannan halaye dai ba wai yana faruwa ne don jahiltar su da cuta ko munafuntar su da aka yi ba ne, a’a, sai don tsananin saninsu da cewa sakamakon bai wuce haka ba.
Ni dai a layin na ukun nake. Domin abin da idanu ya gani ya makale a kan idanun, sai maimaita kansa yake cikin daci da matsuwa, har ya soma lafawa, bayan da na kwana uku, albarkacin Hajiya Hasana mai lallashi na. Inda sai bayan lafawarsa ne na sami idon kokawa. Wannan kuwa ba don komai ba sai don tausayin gazawa ta ga gano hanyar da zan rama wannan cuta da ake ta lafta mini.
1
Add a comment...

BBCHausa

Shared publicly  - 
 
'Kakkabe Boko Haram a Disamba zai wuya' http://bbc.in/1MHf0Li
 ·  Translate
1
Sade Saidu Daura's profile photoharouna gajeren malam filinge gao kkabini's profile photoBadamasi Aliyu Rijiyarlemo's profile photo
7 comments
 
Mudai addu'ar mu akullum ita ce Ya Allah ka kawo mana karshen rikicin Boko Haram a duk fadin Najeriya
Add a comment...

BBCHausa

Shared publicly  - 
 
Iyalan Bello Chindo sun musanta zargin da ake yi masa http://bbc.in/1MH81lm
 ·  Translate
1
Sade Saidu Daura's profile photoUba Umar's profile photoUmar Alassan Kamaru's profile photo
10 comments
 
Agaskiya ya kamata sojojin najeriya susan irin aikina sukeyi
Add a comment...

BBCHausa

Shared publicly  - 
1
Bashiru Bello's profile photo
 
Mane shine ya cancanta
Add a comment...

BBCHausa

Shared publicly  - 
3
jamilu lalo's profile photo
 
Yes he deserved it. he is my favorite player 
Add a comment...
People
In their circles
9 people
Have them in circles
8,920 people
Ibrahim Aminu's profile photo
Abdulazeez Sulaiman's profile photo
Inuwa Daneji's profile photo
Ashiru saleh Baure's profile photo
Johnbiafra Inyari's profile photo
jamilu abdullahi's profile photo
Nuyong Elam's profile photo
Tasiu Garba's profile photo
Abubakar Dabo's profile photo
Story
Tagline
BBC, Hausa, labarai, rahotanni, Nigeria, niger, cameroon, ghana, london, BBC Hausa
Introduction
BBC Hausa Google+: Sada zumunci da wanzar da muhawara mai amfani.Tunatarwa: Ban da Zagi, Batanci da talla a wannan shafi. Tambari da sunan BBC mallakar kamfanin ne. Jama'a ba su da izinin yin amfani da su. Hakan zai kai ga daukar matakin doka.